Thursday, June 4, 2020

GASAR RUBUTUN GAJERUN LABARAI KARO NA BIYAR
Barka da zuwa gasar rubutun kirkira na POWA wadda take gudana a duk karshen wata.
Jigon gasar watan nan na Mayu shi ne TA'ADDANCI.

A karanta wannan jawabin da kuma dokokin gasar a nutse daga bisani kuma sai a rubuta gajeren labari, rubutacciyar waka ko wasan kwaikwayo akan jigon da aka ambata a sama.
Gwarzon da ya zo na daya za a ba shi takardar shaidar karramawa.

Mutum biyun da labaransu suka zo matakin na biyu da na uku za a basu takardar shaidar lambar yabo.

Sauran wadanda suka shiga gasar za a basu alama/shaidar samun damar fafatawa.

Za a zabi labarai uku mafi kayatarwa tare da taskace su don bugawa a littafin gajerun labarai na kungiyar wanda za a yi shi nan gaba.

************************************************

Tsari da Ka'idojin Shiga Gasa:
1. Rubutun zai iya zama gajeren labari, wasan kwaikwayo ko rubutacciyar waka.
2. Duk rubutun da aka shigar dole ya kasance mallakin wanda ya shiga gasar ne kuma ba a taba buga shi a wani wurin ba a baya.
3. Rubutun dole ya kasance a daya daga cikin wadannan harsunan (Hausa/Turanci)
4. Gajerun labarai dole yawan kalmomin su kai 1000 kuma kar su wuce 1500.
5. Rubutacciyar waka dole ta kai layuka 30 kuma kar ta wuce layuka 50.
6. Dukkan labaran su kasance an yi kokarin bin ka'idojin rubutu.
7. Da labari daya kowane mutum zai shiga gasar.
8. Za a tura labarin shiga gasar ta wannan adireshin na kibdau: powaexcos@gmail.com.
9. Akwai dokokin da za a gindayawa wadanda suka yi nasara. Dole sai an aminta da bin su kafin a aiko labari.
10. Idan ba a rubuta taken gasar ba a saman rubutun da aka aiko kamar haka: #POWA2020contest05 alkalai ba za su saurari labarin ba.

Ranar rufe shiga gasa: 31/03/2020, da misalin karfe 5 p.m.

Za a fadi sakamakon a ranar/kafin 11 ga watan Afirilu, 2020.

Allah ya bada sa'a.

Lorem ipsum dolor sit amet, consectetuer adipiscing elit, sed diam nonummy nibh euismod tincidunt ut laoreet dolore magna Veniam, quis nostrud exerci tation ullamcorper suscipit lobortis nisl ut aliquip ex ea commodo consequat.

0 Comments:

Post a Comment

Start Work With Me

Contact Us
JOHN DOE
+123-456-789
Melbourne, Australia

Recent Story

Pages

Featured News