Thursday, June 4, 2020

Shirin Gyara Kayanka
Filin Gyara Kayanka kamar yadda aka saba zai zo da misalin karfe 8:30pm na yammacin yau. Kafin zuwan lokacin ga labarin da za a nazarta don tattaunawa akai. 

MUTUWATA: GAJEREN LABARI

Farkon Labari
Na gama fidda rai da tsammani ga samun rabo, na kuma sallamar cewa ba na daga jerin mutanen da za su yi gamo da katari na samun dace. Ban san ya ake yi ko kuma ya al'amarin yake faruwa ba illa dai kawai a ƙarshe na kan tsinci kaina tsamo-tsamo a hali na aikata laifi ko alfasha.

Kawo yanzu da na ba wa shekaru tamanin baya, ni Baba Adamu ban san yawan laifukan da na aikata ba daga zamanin da nake tashen samarta zuwa yanzu da nake kwance bisa gado na jinyar ajali, bayan da komai da na mallaka ya ƙare a wajen neman maganin cututtukan da suka yi sanadin kwanciyata har na kasance a cikin wannan hali na jinya, tun daga kan cutar dajin dana haɗu da ita a dalilin yawan shan sigari, hawan jini bisa rasa dukiya ta, cuta mai karya garkuwar jiki da na kwaso a yawon sharholiya ta da karuwai, ga ciwon ƙoda da yoyon fitsari, ban da ciwon suga da shi ma likitoci suka ce ina ɗauke da su.

Ina cikin wannan hali ne kwatsam sai ga Malam Muhammadu liman ya shigo duba lafiyata shi ne kuma kaɗai ya waiwaye ni tun bayan da na kwanta wannan jinya. Ya kuwa tarar da ni ina ta sharɓar kuka.

"Ka kwantar da hankalin ka Baba Adamu, ita cuta ai ba mutuwa ba ce, bugu da ƙari duk wanda ka ga ya kwanta jinya to Allah ne yaso shi da rahama saboda ita jinya tana kankare zunuban da mutum ya aikata ne a baya" inji liman.

Bakina na motsa daƙyar cikin jin raɗaɗin zafin ciwon dake ratsa ni nace, "Gafarta Malam...ni da na shafe tsawon rayuwa ta wajen aikata manyan laifuka ga Ubangiji ta ya ma zan kawowa kaina zaton samun rahama da har zan ɗauki wannan ciwo a irin matsayin da ka ambata...ai kawai azaba ta ce aka fara yi mani tun daga nan duniya..."

"Sam kada ka furta haka" Liman ya katse ni, "kuskure ne babba fidda rai ga samun rahamar Ubangiji. Domin kuwa Allah da kansa yana son masu tuba bisa kuskuren da suka aikata masa. Yana da kyau ka sani cewa babu wani shamaki a tsakanin mutum da mahaliccinsa kamar yadda babu hijabi ga addu'ar wanda ya tuba bisa kuskurensa. Muddin ka yi nadama akan laifukan ka to ka nemi yafiyar Ubangiji shi kuma zai gafarta maka".

Da wannan jawabi na Malam Muhammadu na samu karfin gwiwa tare da jin wani sanyi ya ratsa zuciyata saboda fahimtar girman alaÆ™ar dake tsakanin mutum da mahaliccinsa. 

Istigifari na ci gaba da yi tare da zuba ido ina jiran ta inda *mutuwata* za ta sauko gare ni.

Karshen Labari

Shirin namu a wannan rana zai bada dama kamar yadda aka saba don yin sharhi, fashin baki, tsokaci, zakulo kurakurai, jefa tambayoyi ga marubucin labarin, gami da suka ko kalubalantar rubutun (criticism) amma kafin faruwar hakan, wannan karon za mu bi shirin ne daki-daki don gabatar da shirin a cikin tsari. 
Da fari duk wanda yake da abin fada zai fara ne da daukar lamba, Wanda yake a farko shi ne zai fara gabatar da nazarinsa kan labarin kafin mai bi masa wato tsarin nan na first come, first serve.
1
2
3
4
5
Mutane biyar shirin namu zai ba wa damar yin sharhi. Bayan kowane sharhi kuma akwai damar/yiwuwar tafka muhawara kafin a bada dama a na gaba don ya turo na shi. 

A karshe shirin na mu, zai kammala ne da kawo mana darasi na 04 a jerin darussan mu na koyon ka'idojin rubutu.

Lorem ipsum dolor sit amet, consectetuer adipiscing elit, sed diam nonummy nibh euismod tincidunt ut laoreet dolore magna Veniam, quis nostrud exerci tation ullamcorper suscipit lobortis nisl ut aliquip ex ea commodo consequat.

0 Comments:

Post a Comment

Start Work With Me

Contact Us
JOHN DOE
+123-456-789
Melbourne, Australia

Recent Story

Pages

Featured News

Popular Feed